Idan Janaba ta kama mutum,sai yayi wanka sannan yayi sallah.
Idan kuma yanayin rashin Lafiya, Sanyi me tsanani ko idan kamin a gama wankan lokacin Sallah zai fita, toh ana iya yin Taimama a yi Sallah.
Saidai daga baya dole za’a samu ruwa a yi wanka dan ci gaba da sallah.
Janaba tana kama mutum ne idan yayi jima’i mace. Yin jima’i ba yana nufin sai an fitar da maniyyi ba, da zarar kan kaciyarka ta bace a cikin farjin mace, to wankan janaba ya kamaka.
Hakanan idan ka yi bacci ka yi mafarki kana jima’i, ka fitar da maniyyi shima zaka yi wankan janaba.
Hakanan idan ka yi wasa da kanka ka fitar da maniyyi shima sai an yi wankan janaba.