YADDA AKE DAMBUN KIFI
Kayan hadi
– Kifi
– Attarugu
– Albasa
– Tafarnuwa
– Sinadarin dandano
– Garin curry
– Gishiri
– Man gyada
Yadda ake hadawa
– A wanke kifin a gyara shi sosai, sai a dora tukunya a kan wuta, a zuba kifin da kayan kamshi da kayan dandano da tafarnuwa da sauransu.
– A zuba ruwa kadan sai a bar shi ya dan dahu kadan, sai a sauke.
– A kwashe ya sha iska sai a saka a turmi a daka shi har sai ya daku yadda ake so, a kwashe a ajiye a gefe.
– Sai a daka attarugu da albasa a hada da kifin a gauraya sosai.
– Zuba sinadarin dandano da garin curry a ciki sai a jujjuya su hadu sosai.
– A dora tukunya a wuta sai a zuba man gyada kadan a soya yadda ake so.
Shi ke nan sai ci.