Darajar Naira ta dan farfado a kasuwar canji ranar Talata.
An sayi dala akan Naira 1,725 ranar Talata, idan aka kwatanta da Yanda aka sayi Dalar akan Naira 1,730 ranar Litinin, za’a iya ganin cewa darajar Nairar ta dan farfado da Naira 5.
Hauhawar farashin dala dai na daga cikin abubuwan dake kara tsadar kayan abinci a Najeriya.