Friday, July 17
Shadow

Muna nan akan bakarmu na baiwa shugaba Tinubu shawarar ya ci gaba da kara kudin man fetur>>IMF

Hukumar bayar da lamuni ta Duniya tace bata canja ba, har yanzu tana nan akan bakanta cewa shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur dana dala.

Hukumar tace ta hakane ‘yan Najeriya zasu samu saukin rayuwa daga matsin tattalin arzikin da suke fama dashi.

Karin farashin man fetur dai yasa kayan masarufi sun tashi sama sosai inda talakawa ke cin abinci da kyar.

Lamarin ya jawowa gwamnati tofin Allah tsine tsakanin Talakawa.

Hakanan an sha zargin hukumar ta IMF da bankin Duniya da bayar da shawarwarin dake jefa kasashe da yawa cikin wahalar rayuwa.

Karanta Wannan  Har Majalisa Sanata Natasha Akpoti ta zo mana da Mijinta suka sumbaci juna, su rasa inda zasu je su yi hakan sai a gaban mu, Tana zargin Sanata Godswill Akpabio da nemanta ne kawai dan daukar hankalin mutane>>Inji Majalisar Dattijai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *