Wata matar aure me suna Comfort Olajumoke Olalere Tinubu ta kashe mijinta ta hanyar caka masa wuka ya mutu bayan da gaddama ta barke a tsakaninsu.
Lamarin ya farune a Gbeyi dake yankin Adegbayi a Ibadan jihar Oyo da misalin karfe 10 na daren Laraba, 30 ga watan October 2024.
Shekaru 3 kenan da aurensu kuma suna da yara 2.
TheNation ta ruwaito cewa matar me shekaru 33 ta kulle mijinta, Olusegun a dakinsu bayan da suka yi fada wanda daga baya abin ya kazance da ya kai ga har ta caka masa wuka ya mutu.
Zuwa yanzu dai ‘yansanda na bincike akan lamarin.