Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya bayyana cewa, sumar da matasa 6 suka yi a kotu karyace kawai dan su jawo hankalin mutanene.
Saidai yace duk da haka an baiwa matasan taimakon gaggawa wanda hakan ke nuna kokarin ‘yansanda wajan ganin sun baiwa wanda suke tsare dasu kulawa.
Yace kuma maganar shekarun yaran idan dai mutum ya kai shekarar aikata laifi karancin shekarunsa basa hana a hukuntashi kuma haka dokar take koda a kasar Ingila ne.
Yace wasu daga cikin laifukan da ake zargin yaran da aikatawa sun hada da lalata dukiyar ‘yan kasa da kuma barazana ga tsaron kasa.
Ya kara da kira ga mutane da kada su nuna goyon bayan wani bangare kuma hukumar ‘yansanda zata tabbatar ta bayyana duk abinda ke faruwa ba tare da boye komai ba.
Sanan ya bayar da tabbacin cewa hukumar ‘yansandan zata ci gaba da aiki bisa kwarewa da bin doka da oda.