Tuesday, May 19
Shadow

Hotuna: Matar aure ta càkàwà mijinta wuka ya mùtù bayan da gardama ta barke tsakaninsu

Wata matar aure me suna Comfort Olajumoke Olalere Tinubu ta kashe mijinta ta hanyar caka masa wuka ya mutu bayan da gaddama ta barke a tsakaninsu.

Lamarin ya farune a Gbeyi dake yankin Adegbayi a Ibadan jihar Oyo da misalin karfe 10 na daren Laraba, 30 ga watan October 2024.

Shekaru 3 kenan da aurensu kuma suna da yara 2.

TheNation ta ruwaito cewa matar me shekaru 33 ta kulle mijinta, Olusegun a dakinsu bayan da suka yi fada wanda daga baya abin ya kazance da ya kai ga har ta caka masa wuka ya mutu.

Zuwa yanzu dai ‘yansanda na bincike akan lamarin.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya bayar da Umarnin a dauki matasa 130,000 aiki dan su shiga daji su gama da 'yan Bìndìgà da ake fama dasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *