Monday, December 16
Shadow

Kalli Bidiyo: Yanda wata Daliba a kasar Iran ta tube kayanta, ta yi Tumbur, haihuwar uwarta a tsakiyar makaranta saboda an mata hukunci kan shigar banza da ta yi

Wata daliba a jami’ar Tehran’s Science and Research University dake kasar Iran ta dauki hankalin Duniya saboda tabarar da ta yi.

Sanin kowane kasar Iran kasar Musulunci ce da bata wasa idan mata suka yi shigar banza ana hukuntasu sosai.

Wannan dalibar hukunci ya hau kanta inda jami’an tabbatar da da’ar dalibai na jami’ar Tehran’s Science and Research University suka hukuntata saboda shigar banza da ta yo ta je makarantar.

Saidai abin bai mata dadi ba inda kuwa nan take ta cire kayanta gaba daya daga ita sai rigar mama sai dan kamfai watau Pant.

Ta rika cire pant dinta tana nuna Al’aurarta watau irin abinnan dai dake nuna cewa in kashe ta za’a yi saidai a kasheta gashi ma ta yi tsirara gaba daya haihuwar uwarta.

Karanta Wannan  Duk Abunda ya faru a Kano, Tinubu ne sila>>Inji Atiku

Tuni dai aka kamata aka tafi da ita zuwa asibitin mahaukata dan mata gwajin lafiyar kwakwalwa.

Tuni Kungiyoyin dake ikirarin kare hakkin bil’adama na kasashen yamma suka fara kiran da a saketa bata aikata laifin komai ba.

A cewarsu jikinta ne ba na wani ba kuma bai kamata a tursasa mata kan kalar kayan da ya kamata ta saka ba.

Karanta Wannan  Tonon Silili, Kalli Hotuna: An Bayyana 'yan matan kakakin majalisar tarayya, Godswill Akpabio har su 5

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *