Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, mutane nata tambayar wai shin da shine shugaban kasa,wane matakai zai dauka na kawo karshen rayuwar kunci da ‘yan Najeriya ke ciki?
Atiku yace maganar gaskiya ba shine shugaban kasa ba dan haka Tinubu ne kuma shi ya kamata a rika damu akan ya fito da hanyoyin gyara dan samawa mutane saukin rayuwa.
Atiku yace kuma yana baiwa Tinubun shawarar ya dauki wasu daga cikin tsare-tsare ln da yaso yayi da yaci Shugaban kasar Najeriya.
Atiku yace amma duk da haka bari ya dan amsa wannan tambaya kadan.
Yace tabbas an sanshi yana daga cikin masu fafutukar a cire tallafin man fetur.
Amma da shine shugaban kasa, ba zai cire tallafin man fetur a rana daya ba irin yanda Tinubu yayi.
Yace zai tsaya ya fara la’akari da matsalolin kasarnan sannan ya tuntubi masu ruwa da tsaki akan harkokin al’umma.
Sannan zai yiwa kamfanin mai na kasa, NNPCL Garambawul, zai sayar da matatun man Najeriya dan su samu yin aiki yanda ya kamata.
Yace kuma za’a rika cire tallafin a hankali har a kammala cireshi gaba daya, yace a lokacin da suka yi mulki sun fara cire tallafin man fetur din a hankali amma gwammatin da ta gajesu ta yi watsi da tsarin.
Yace a kasashen da aka ci gaba irin kasashen Turai da sauransu, sukan dauki shekaru 5 ana cire tallafi a hankali har a cireshi gaba daya.