Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa ya amince da shawarar da dan takarar shugaban masa na jam’iyyar PDP a shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bashi ta cewa ya rika tausayawa da tallafawa talakawa saboda matsin tattalin arzikin da ake ciki.
Shugaban kasar ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga a sanarwar da ya fitar ta mayar da martani ga Atikun akan shawarar da ya baiwa Tinubun ta cewa ya dauki tsare-tsaren sa dan gyara kasa da fitar da mutane daga matsin rayuwar da suke ciki.
Tinubu yace tsare-tsaren na Atiku tuni ‘yan Najeriya suka ce basa so tunda basu zabeshi kumama ba’a gwadasu aka ga ko suna aiki ba dan haka ba zai dauka ba.
Saidai a cikin bayanan na Atiku akwai inda yacewa Tinubu ya tausayawa talakawa da tallafa musu dan samun saukin Rayuwa.
Tinubu yace ya yadda da wannan shawara ta Atiku kumama Tuni a cikin tsare-tsaren gwamnatinsa akwai wadannan shirye-shiryen na tallafawa talakawa da basu tallafin.