Monday, December 9
Shadow

Tsadar Rayuwa tasa Tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ya ragu da kaso 60 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa tafiye-tafiye zuwa kasashen waje daga Najeriya ya ragu sosai saboda tsadar rayuwa.

Mutanen da aka saba gani a filayen jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja da na Murtala Muhammad dake Legas sun ragu sosai da kaso 60 cikin 100.

Rahoton na jaridar Leadership yace hauhawar farashin dalar Amurka na daga cikin abubuwan da suka jawo wannan matsala.

A baya dai da rayuwa ke da sauki ana samun ‘yan Najeriya dake zuwa kasashen waje yin hutun karshen mako ko hutun nishadi da sauransu.

Rahoton yace a shekarar 2023 mutane miliyan 2.4 ne suka fita daga Najeriya zuwa kasashen waje inda a shekarar 2024 da muke ciki kuma mutane 816,000 me suka fita.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda wasu sojoji dake kwance a gadon asibiti ke tika rawa suna shakatawa

Rahoton yace tikitin jirgin sama zuwa kasar Amurka wanda a baya ana sayansa akan Naira 350,000 a yanzu ya koma Naira miliyan 2.7 zuwa Naira Miliyan 3.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *