Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta kasa,EFCC ta kama tsohon Gwamnan jihar Delta,Efeanyi Okowa akan zargin Almundahanar kudi.
Ana zargin tsohon gwamnan da karkatar da Naira Tiriliyan 1.3.
Kudin dai an bayyanasu a matsayin kaso 13 dinnan da ake warewa jihohin da ake hako man fetur a cikinsu.
Wata majiya data san da lamarin tace an karkatar da kudadenne a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023.
An kama Okowa ne a ranar Litinin a Birnin Fatakwal na jihar Rivers a yayin da ya je ofishin EFCC amsa gayyatar da suka masa.
Hakanan ana kuma zargin tsohon gwamnan da karkatar da wasu kudaden na daban da suka kai Naira Biliyan 40