Gwamnatin jihar Sokoto ta kama wata budurwa don tayi kira ga Gwamnan jihar kan halin rashin tsaron da ya addabi garinsu a wani bidiyon da ya yita yawo na budurwar a kafofin sada zumunta inda budurwar take kiran sunan Gwamnan kai tsaye akan lamarin rashin tsaro.
Abba Pantami ya samu sahihin labarin cewa a jiya Lahadi Gwamnatin jihar ta tura aka kama budurwar inda a yau Litinin ta gabatar da ita a gaban kotu kan zargin yiwa Gwamnan jihar rashin kunya.
A yanzu haka budurwar tana tsare a hannun hukuma a jihar Sokoto, sunan budurwar Hamdiya Sidi dake karamar hukumar Wurno jihar Sokoto, garin nasu yana daya daga cikin yankunan dake fama da matsalolin rashin tsaro.
Daga Shafin Dokin Karfe TV