Tuesday, May 19
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin jihar Sokoto ta kama wata budurwa dòn tayi kira kan mátsalar tsaròɲ garinsu

Gwamnatin jihar Sokoto ta kama wata budurwa don tayi kira ga Gwamnan jihar kan halin rashin tsaron da ya addabi garinsu a wani bidiyon da ya yita yawo na budurwar a kafofin sada zumunta inda budurwar take kiran sunan Gwamnan kai tsaye akan lamarin rashin tsaro.

Abba Pantami ya samu sahihin labarin cewa a jiya Lahadi Gwamnatin jihar ta tura aka kama budurwar inda a yau Litinin ta gabatar da ita a gaban kotu kan zargin yiwa Gwamnan jihar rashin kunya.

A yanzu haka budurwar tana tsare a hannun hukuma a jihar Sokoto, sunan budurwar Hamdiya Sidi dake karamar hukumar Wurno jihar Sokoto, garin nasu yana daya daga cikin yankunan dake fama da matsalolin rashin tsaro.

Karanta Wannan  ALLAH SARKI: Umar Ya Tafi Ziyarar Sallah Daga Miltara Zuwa Daura, Sai Allah Ya Yi Masa Rasùwà Sakàmakon Hadariñ Mota A Jiya Asabar

Daga Shafin Dokin Karfe TV

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *