Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP,Alhaji Atiku Abubakar ya mayarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu martani kan maganar da ya masa ta cewa tsare-tsaren shi da yake baiwa Tinubu shawarar ya dauka ba’a gwadasu an ga yanda suke aiki ba.
Atiku yace gaggawa wajan daukar matakai ba tare da taka tsantsan ba ne da gwamnatin ‘yan koyo ta Tinubu ke yi ne ya jefa kasarnan cikin wahala.
Atiku yace abin mamaki ne ace bayan da ya yi kiran a kawo gyara,Tinubu ya rasa irin gyaran da zai kawo saidai yace a yi addu’a.
Atiku yace a zamanin mulkinsu da Obasanjo ke shugaban kasa Najeriya ce ta daya a wajan ci gaba a kaf Nahiyar Africa.
Saidai yace a yanzu Gwamnatin Tinubu ta mayar da Najeriya kasa ta 4 wajan ci gaba a Afrika.
Yace kuma maganar haraji da Tinubu ke son kakabawa mutane ba itace mafita ba dan kuwa kasashen da suka ci gaba sassauta haraji suke ba tsanantawa ‘yan kasa ba.
Atiku ya kuma ce tsare-tsaren gwamnatin Tinubu babu abinda suke kawowa Najeriya sai Wahala.
Yace kuma maganar zabe kowa yasa ba faduwa zabe yayi ba, murdiyace aka yi.