Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin fara bincike kan yanda aka tsare kananan yara masu zanga-zanga wanda aka gurfanar a kotu.
A baya dai, an gurfanar da kananan yaran a kotu su 32 inda suka rika faduwa saboda tsananin yunwa, saidai shugaban ‘yansandan ya bayyana cewa faduwar karyace kawai dan neman magane.
Amma a sabuwar sanarwar da kakakin ‘yansandan, Muyiwa Adejobi ya fitar yace shugaban ‘yansandan yace a yi bincike dan gano ko an aikata ba daidai ba yayin tsaron yaran.
Sannan ya sha Alwashin daukar mataki da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi yayin kamawa ko kula da yaran.