Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta dakatar da dauke bidiyo daga yanar gizo a kasar.
Hakan na zuwane bayan da jami’in gwamnatin kasar Baltasar Engonga ya fallasa a Duniya inda aka ganshi yana lalata da mata daban-daban a wasu biyoyi guda 400 da suke ta yawo a kafafen sada zumunta.
Ana ganin wannan matakin yunkuri ne na gwamnatin kasar na dakile yada yada Bidiyon badalan na jami’in Gwamnatin.
A baya,hutudole ya kawo muku cewa, daya daga cikin matan da yayi lalata dasu ta kashe kanta saboda kunyar bayyanar Bidiyon nasu da surutun da mutane me mata.