Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya taya Donald Trump murna, inda ya ce a shirye yake su ci gaba da aiki tare domin inganta alaƙa tsakanin Najeriya da Amurka.
Ya ce, “idan muka haɗa kai, za mu inganta tattalin arziki da zaman lafiya da magance matsalolin da al’umarmu ke fuskanta,” kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya sanar.
Trump ne dai ya sanar da samun nasararsa a jawabinsa ga magoya bayansa, inda ya ce ya samu gagarumar nasara.
Tinubu ya kuma yaba wa Amurkawa bisa yadda suka gudanar da zaɓen cikin lumana.
Tinubu ya ce kasancewar Trump ya taɓa yin mulkin ƙasar, dawowarsa a matsayin shugaban ƙasar na 47 zai zo da gagarumar sauyi a tattalin arziki da ƙarin haɗin kai tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka.