Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya taya shugaban kasar Amurka, Donald Trump murnar lashe zaben shugaban kasar.
A sakon da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta, Atiku ya bayyana Tsarin Dimokradiyya a matsayin mafi dacewa duk da yana da matsalolinsa.
Atiku ya kuma bayyana cewa irin gwagwarmayar da Donald Trump ya sha kamin ya zama shugaban kasar darasine babba da ya kamata a lura dashi.
Hakanan Atiku ya kuma taya Donald Trump da mutanen kasar Amurka murnar nasarar zaben inda yace yana fatan Donald Trump din zai taimaka wajan aiwatar da zaben gaskiya a Najeriya da sauran kasashen Duniya.