Babban bankin Najeriya ya nuna cewa,Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Triliyan 4.4 wajan biyan bashi a watanni 3 na biyu na wannan shekarar watau tsakanin watannin April, May da June.
Jimullar kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe a cikin wadannan watanni 3 Naira Tiriliyan 6.8 ne gaba daya wanda daga ciki ne aka cire Naira Tiriliyan 4.4 aka biyawa Najeriyar bashi watau dai Naira 2.4 ne suka yi saurawa gwamnati ta gudanar da sauran ayyukan kasa dasu.
Hakan na nufin kaso 64.7 cikin 100 ne gwamnatin ta kashe wajan biyan bashi daga cikin kudaden shigarta.
Hakan kuma na nufin Najeriya ta kashe fiye da abinda take samu a tsakanin wadannan watannin.
Jimullar bashin da ake bin Najeriya dai ya kai Naira 121.67.