Friday, July 17
Shadow

Muna tabbatar da ingancin man fetur din da ake shigo dashi Najeriya>>Gwamnati ta mayarwa da Dangote Martani

Hukumomin SON, da NMDPRA sun mayarwa Dagote Martanin cewa duk man fetur din da za’a shigo dashi Najeriya sai sun tabbatar da ingancinsa.

Hukumomin sun bayyana hakane bayan da Dangote yayi zargin cewa ‘yan kasuwar man fetur na zuwa kasashen waje dan siyo man fetur da bashi da inganci cikin kasarnan mai makon su sayi na matatar man fetur dinsa.

Dangote dai ya kai ‘yan kasuwa da suka hada da A.A Rano, AY Shafa,da kamfanin man fetur na kasa NNPCL kotu inda yake neman kotu ta hanasu shigo da man fetur cikin kasarnan har sai idan matatarsa ta kasa samar da man fetur din.

Karanta Wannan  Kalli Hoto: Tsohuwar 'yar kwallon Najeriya da Tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad ya dauki nauyinta zuwa kasar Amurka aka mata aiki ta koma Namiji na neman taimakon Naira Miliyan 69.7 dan a mata karin aikin da zata rika haihuwa

Saidai A.A Rano da AY Shafa sun zargi Dangote da kokarin kare kasuwancinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *