Monday, December 16
Shadow

Wata Sabuwa: Iyalan marigayi Shugaban sojojin, Lagbaja sun yi zargin cewa kasheshi aka yi

Kanin Mahaifin marigayi shugaban sojojin kasa na Najeriya, Lt. General Taoreed Lagbaja me suna Pa Tajudeen Lagbaja ya bayyana cewa, yana dana sanin sayarwa shugaban sojojin fom din shiga soja da yasan hakan zai yi sanadiyyar mutuwarsa.

Wasu Dangin shugaban sojojin sun yi zargin cewa an kashe shi ne ta hanyar tsubbu wanda ya samo Asali daga wani rikicin Fili a mahaifarsa.

Kanin mahaifin nasa yace mutuwar data dauki shugaban sojojin, shi ya kamata ace ta dauka.

Ya yabeshi a matsayin wanda ya rika tallafawa mutane kowa da kowa.

Karanta Wannan  Gwamnati ta sake kara farashin man fetur zuwa Naira 1070 akan kowace lita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *