Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya karbi bakuncin Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso a gidan gwamnati dake Umuahia.
Tattaunawar tasu ta ta’allaka ne kan siyasar kasa da kuma makomar Najeriya. A wani biki na musamman wanda Gwamna Otti ya karrama Sanata Kwankwaso da lambar yabo kan irin gudunmawar da ya bayar ga al’umma, a zamaninsa na Mulki da kuma bayan Mulki.
Saifullahi Hassan