Monday, December 16
Shadow

Hukumar shari’a ta hukunta ma’aikatanta takwas a jihar Kano

Hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Kano a arewacin Najeriya ladaftar da wasu ma’aikatanta takwas ciki har da alkalai.

Wani kwamitin ladaftarwa na hukumar ne ya bayar da shawarar ɗaukar matakin bayan kammala bincikensa kan ƙorafe-ƙorafen da wasu suka gabatar waɗanda suka haɗa da zarge-zargen karɓar rashawa.

Kwamitin karɓar korafe-korafen jama’a na hukumar kula da harkokin shari’ar ya ɗauki matakin ladaftawar ne kan ma’aikatan shari’a su takwas ciki har da alkalan kotunan majisteret.

Kakakkin hukumar Baba Jibo Ibrahim ya ce bincike ya gano yadda wani alkalin kotun majistare ya gudanar da wata shari’a ba tare da an rubuta ta ba, abin da ya saba dokokin shari’a.

Karanta Wannan  Hotunan muggan makamai na Naira Biliyan 13.9 da hukumar Kwastam ta kama za'a shigo dasu Najeriya

Bayanai na cewa an jima ana kokawa da jami’an kotu a jihar game da yadda suke karbar toshiyar baki da sauran laifuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *