Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa yana sane da ana shan wahala a Najeriya kuma yana kokarin kawo sauyi amma sai an yi hakuri dan ba za’a ga wannan sau yi da gaggawa ba.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin sakataren Gwamnatin tarayya, Senator George Akume a wajan taron zagayowar ranar haihuwar Pastor Tunde Bakare inda ya cika shekaru 70 da haihuwa.
Shugaban ya kuma bayyana Fasto Tunde Bakare a matsayin gwarzo wanda ya bar tarihi me kyau wanda ba za’a manta dashi ba.