Monday, December 9
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 19 wajan kula da jiragen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a cikin watanni 15 da suka gabata

An kashe akalla Naira N19.43bn wajan kula da jiragen sama na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a tsakanin watan July 2023 zuwa September 2024.

Shafin GovSpend ne dake saka ido kan yanda gwamnati ke kashe kudadenta ya wallafa wadannan bayanai.

Hakanan shafin yace a shekarar 2024, gwamnati ta ware Naira N13.55bn dan kula da jiragen na shugaban kasa.

Hakan na zuwane dai a yayin da mutane da yawa a Najeriya ke fama da wahala wajan samawa kansu abinci.

Karanta Wannan  Bidiyo: Kalli Yanda dubban musulmai suka yi Sallar Idi a Birnin Moscow na kasar Rasha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *