Kungiyoyin fafutuka 51 dake ikirarin yaki da rashawa da cin hanci sun nemi hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kama shugaban jam’iyyar APC, Dr. Umar Abdullahi Ganduje kan zargin Rashawa da cin Hanci.
Kungiyoyin sun rubuta takardar neman a kama Gandujene ranar November 4, 2024 inda ita kuma hukumar EFCC ta karbi takardar ranar November 7, 2024.
A lokacin da yake rike da mukamin gwamnan Kano,an zargi Dr. Umar Abdullahi Ganduje da cin hanci da rashawa ta fannoni daban-daban.
Akwaidai shaidu 143 wadanda suke a shirye su bayar da shaida akan zargin cin hanci da rashawa na Ganduje wadanda suka hada da ma’aikatan kananan hukumomi da ‘yan canji da tsaffin ma’aikatan banki.
Shuwagabannin kungiyoyin fafutukar da suka kai wadannan bukatu sun hada da Dr. Johnson Nebechi, Comrade Umar Ideresu.
A shekarar 2018 ne jaridar DailyNigerian ta wallafa bidiyon da ya nuna gwamna Ganduje na saka daloli a Aljihu inda a shekarar 2023 kuma EFCC ta gayyaceshi amma bai amsa gayyatar ba.
Kungiyoyin sun nemi EFCC ta gaggauta kamawa da hukunta Ganduje da kuma kwato kudaden da ake zarginsa da sacewa.