Wannan wata mata ce da ta ke a kasar Amurka inda take aiki ana biyanta Naira Dubu 40 duk awa daya.
Tace tana aiki ne a babban shagon sayayya na Amazon inda take aikin dare.
Da yawa dai sun bayyana sha’awar aikin nata.
Saidai wasu na ganin tsadar rayuwa da ake fama dashi a Amurka zai iya lakume kudaden da take samu.