Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya karbi mulkin Najeriya a yayin da take cikin wahalar rashin tabbas na tattalin arziki.
Shugaban yace shiyasa ya dauki matakai tsaurara musamman a bangaren kudi dan ganin ya kawo ci gaba.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan rantsar da zababben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo inda mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilceshi.
Yace a yanzu saboda matakan da ya dauka, kasar ta dauki hanyar ci gaba da nasara.