Rahotanni daga Legas na cewa, gawar marigayi shugaban sojoji, Lt. Gen. Taoreed Lagbaja ta isa Jihar inda za’a yi jana’izarsa.
Gawar ta sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas din da safiyar ranar Alhamis.
A ranar Larabar data gabata ne dai gwamnatin tarayya ta tabbatar da mutuwar shugaban sojojin.
Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da cewa ranar November 15, 2024 za’a yi jana’izar marigayin a makabartar sojoji dake Abuja