Wani magidanci daga jihar Ogun, Enitan Awoyemi dan kimanin shekaru 41 ya buga caca inda aka biyoshi bashin Naira Miliyan daya.
Ganin cewa ba zai iya biyan kudin ba ne yayi karyar cewa an yi garkuwa dashi inda ya kira matarsa ya gaya mata.
Matar ta kira jami’an tsaron Amotekun inda suka fara bincike.
Kwamandan Amotekun din a jihar, Brigadier General Alade Adedigba (retd.) Ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun gano cewa, Enitan karya yayi ba’a yi garkuwa dashi ba.
Yace sun ganoshi yana kokarin kashe kansa inda yace ya sha maganin kwari amma sun kaishi asibiti idan ya warke zasu mikashi wajan ‘yansanda.