Ana gane mace ta balagane ta hanyar canje-canjen dake faruwa a jikinta.
Yawanci mata suna balaga ne a tsakanin shekaru 9 zuwa 13, Inda suke Riga maza balaga da shekaru 2.
Ga alamun dake nuna mace ta balaga kamar haka:
- Girman nonuwa: Nonuwan yarinya zasu fara girma suna kara fitowa wake suna girma.
- Zafin Nono: Saboda girman da suke yi, nonuwan yarinyar zasu Dan rika mata zafi ko kaikai.
- Warin Jiki: Saboda zuwan balaga, yarinya zata iya fara warin jiki.
- Fitar Gashi a Hamata da Gaba: Gashin hamatarta Dana gabanta zasu fara fita suna kara kauri suna murdewa.
- Fara Jinin Al’ada: Yarinya zata iya fara jinin Al’ada.
- Majinar Farji: Gaban yarinyar zai fara fitar da ruwa me yauki.
- Kurajen Fuska: Yarinyar zata iya yin kurajen fuska Saboda canjawar da jikinta take.
- Zata iya kara kiba kuma nauyin jikinta zai karu idan balaga ta so mata.
- Girman Kugu: Kugunta zai bugs ya kara girma.
- Tsukewar Murya: Muryarta zata kara sirancewa.