Friday, December 6
Shadow

Ya ake gane daukewar jinin haila

Ana gane daukewar jinin hailane ta hanyoyi kamar haka:

Yawan jinin da kike zubarwa zai ragu, a yayin da kika lura yawan jinin da kike zubarwa ya ragu to kinzo karshe ko kina gab da gama jinin hailarki.

Canjawar Kalar Jini: A yayin da jinin hailarki ya zo karshe, kalar jinin da kike zubarwa zai canja, zai zama kalar brown ko ruwan anta.

Alamomin jinin Al’ada da kike ji zasu kau, alamomin ciwon Mara, zazzabi ko rashin jin dadin jikinki da kike a yayin jinin Al’ada zasu kau

A yayin da kika gama jinin Al’ada, jinin zai tsaya gaba daya. A farkon fara jinin al’adarki zaki iya ganin jini Pink, idan ya kai tsakiya zai iya komawa jaa watau red, hakanan idan ya zo karshe, zai iya komawa light Brown, a yayin da kika gama gaba daya, zaki ga farin ruwane kawai yake fita daga gabanki.

Karanta Wannan  Ya ake gane mace ta balaga

Ya kamata a ce ki rika girgawa daga ranar da kika fara jinin Al’ada zuwa ranar da zaki gama gaba daya, zaki iya yin amfani da calendar dan samun saukin yin kirgen Saboda ki San yawan kwanakin jinin al’adarki.

Yawanci jinin Al’ada yana faruwa ne a cikin kwanaki 3 zuwa 8, amma akan samu masu yin kwanaki 5 da yawa, hakanan jinin yakan zuba dayawa ne a kwanaki 2 na farko.

Idan baki ga jinin al’adarki ba a cikin watanni 3 ko kwanaki 90 ba kuma ba ciki gareki ba, ba shayarwa kike ba, to ki gaggauta ganin likita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *