Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi.
Hukumar tace an kashe sojojin ne dake rundunar Operation UDO KA da aka kai Obikabia.
Tace akwai kuma farar hula 6 da suma aka kashe a yayin harin.
Kakakin hedikwatar tsaro, Majo Janar Edward ne ya bayyana hakan inda yace zasu tabbatar sun rama wannan kisan da aka musu.
Hukumar sojin tace maharan sun je wajanne a motocin Prado 3 dake da bakin gilashi sannan akwai wasu kuma a yankin da suma suka farwa sojojin.