Wednesday, December 10
Shadow

Mugunta ko cin Amana? Ji yanda shugaban wani kauye a jihar Katsina ya karbi cin hancin Naira dubu dari bakwai(700,000) ya amince aka kaiwa mutanen kauyensa hari har aka kash-she 30

Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Umar Dikko Radda ya bayyana yanda wani shugaban kauye ya karbi Naira dubu dari bakwai ya amince aka kai hari akan kauyenshi wanda yayi sanadiyyar kisan mutane 30.

Gwamnan yace an samu hakanne a Guga dake Bakori.

Ya kara da cewa ba zasu kyale ko wanene aka samu da hannu a harkar ‘yan Bindigar ba.

Saboda rayuwar mutanen jihar tafi ta mutum daya ko wanene shi.

Karanta Wannan  Ana harbi ko aka kàshe mutum daya zamu ajiye duk wasu bukatu zamu koma neman sai Tinubu ya sauka daga mulki>>Inji Masu Zàngà-zàngà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *