Wasu daga cikin sojojin Najeriya dake yaki da kungiyar Boko Haram a dajín Sambisa dake jihar Borno sun koka da yanda aka barsu suka da de a dajin ba tare da canjasu ba.
Sunce tun shekarar 2018, watau shekaru 6 kenan har yanzu ba’a canjasu an kai wasu wajan ba.
Sojojin sunce dadewar da suka yi a wajanne yasa gwiwarsu ta yi sanyi da yaki da kungiyar Boko Haram har take samun galaba a kansu.
Sannan sunce matansu dake gida sun fara yin lalata da abokansu sojoji da kuma fararen hula saboda dadewar da suka yi basu gansu ba.
Sojojin sun yi rokon cewa wannan dadewa da aka bari suka yi a fagen daga ta sabawa dokar aikinsu dan haka suke kiran manyansu dasu canjasu ko sun samu sa’ida.
Sojojin sun bayyana hakane a wata hira da jaridar Sahara Reporters saidai basu yadda an fadi sunayensu ba dan gudun bita da kulli.