Friday, December 6
Shadow

Yadda ake gyaran fuska da nescafe

Nescafe ko kuma nace Coffee na da matukar amfani sosai wajan gyaran fuska.

Wasu daga cikin abubuwan da Nescafé ko Coffee kewa fuska sun hada da:

Kawar da tattarewar fuska da alamun tsufa.

Maganin kurajen fuska.

Maganin fatar dake tattarewa karkashin ido.

Kawar da duhun fuska wanda dadewa a rana ke kawowa.

Yana sa hasken fuska.

Yana cire matacciyar fatar fuska.

Yana bada garkuwar kamuwa da cutar daji ta fata.

Yana kawar da tabon kurajen fuska, yana maganin kumburin fuska.

Yadda ake gyaran fuska da nescafe

Ana kwaba garin Nescafé da ruwa a shafa a fuska a bari yayi mintuna 15 zuwa 20 sai a wanke da ruwan dumi.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da kwai

Domin kawar da tattarewar fatar kasan ido kuwa, Ana samun garin Nescafé a hada da man zaitun a kwaba, a shafa a kasan ido da sauran fuska a bari yayi mintuna 15 zuwa 20, kamin a wanke da ruwan dumi.

Dan kawar da kuraje, tattarewar fuska da duhun fuska, da sa hasken fuska, sai a samu garin Nescafé ko coffee, a hada da zuma a kwaba a shafa a fuska a bari yayi mintuna 15 zuwa 20 sai a wanke da ruwan dumi.

Ana kuma iya hada garin Nescafé da kurkur da Yegot a shafa a fuska shima a bari yayi mintuna kamar 15 zuwa 20 haka sai a wanke da ruwan dumi.

Ana sa Nescafé ko garin coffee babban cokali 1, sai yegot rabin babban cokali, sai kurkur rabin karamin cokali.

Karanta Wannan  Maganin kurajen fuska

Duka wadannan za’a yine na tsawon akalla sati biyu.

Sannan akwai namu hadin na Nescafé wanda muka yi na musamman dake sanya hasken fuska, kawar da kuraje, da kawar da tattarewar fuska, data kasan ido, idan ana bukata Naira dubu goma ne(10,000) a mana magana ta whatsapp da wannan lambar, 09070701569. Muna aikawa duka jihohin Najeriya, amma ke zaki biya kudin mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *