A jiyane muka samu labarin cewa, kotu a Abuja ta kwace wasu gidaje 753 daga hannun wani tsohon ma’aikacin gwamnati inda ta mallakawa gwamnatin tarayya su.
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ce ta bayyana haka a wata sanarwa data fitar inda tace kamen shine mafi girma da aka taba yi a tarihinta.
Saidai bata bayyana sunan jami’in gwamnatin data kwace wadannan kadarorin daga hannunsa ba.
A sabon rahoton da muka samu, Mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ne aka kwace wadannan gidaje daga hannunsa.
Emefiele dai tun hawan mulkin shugaba, Bola Ahmad Tinubu ake bincikensa da laifuka daban-daban.