Sunday, January 5
Shadow

Ya ake farantawa saurayi rai

A na farantawa saurayi raine ta hanyar damuwa da shi.

Damuwa dashi na nufin damuwa da abinda yakeyi musamman Wanda ya baki labari, idan ya baki labarin Abu, kasuwanci ne, aiki ne, ko wani Abu da yakeyi, ki nuna damuwa akai, ki rika tambayarsa ya ake ciki da abunnan daga lokaci zuwa lokaci.

Kuma kamar yanda idan ya yabeki kike jin dadi, idan ya gaya miki yana sonki kike jin dadi, to haka shima idan kina son ki faranta masa, ki rika yabonsa, da gayamai irin soyayyar da kike masa.

Yana da kyau ki rika nuna kishinsa, amma kada ki wuce gona da iri, hakanan ki rika tambayarsa ‘yan gidansu da yanda suke.

Karanta Wannan  Kada Ki Jira Har Sai Namiji Ya Zo Neman Aurenki, Idan Kin Yaba Da Halinsa, Za Ki Iya Tallata Masa Kanki Don Ya Aure Ki, Ra'ayin Zainab 'Yar Adamawa

Ki rika nuna mai kaguwa da soyuwar kasancewa tare dashi da son ya aureki dan Ku yi rayuwa tare.

Idan ya miki kyautar dubu 1, ki nuna jin dadi da mai godiya kamar ya miki kyautar dubu 10, idan ya miki kyautar dubu 10, ki nuna jin dadi kamar ya miki kyautar dubu 100, hakan zaisa ki kara kima da soyuwa a ranshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *