Saturday, January 4
Shadow

Mutane 171 sun mutu bayan hadarin jirgin sama

Hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu ta ce aƙalla mutum 177 ne suka mutu a hatsarin jirgin saman ƙasar bayan da wani jirgin saman fasinja ya kauce daga titinsa yayin da yake sauka a filin jirgin sama a Koriya ta Kudu.

Jirgin kirar Boeing 7-3-7 ya sauka kenan, bayan dawowa gida daga Bangkok na kasar Thailand, dauke da fasinjoji 175 da ma’aikatansa shida.

Saukar ta sa ke da wuya ne ya kwace ya saki titinsa ya kutsa ta cikin wani gini, kana ya kama da wuta.

Shaidu sun ce sun ji karar fashewar wani abu mai karfi bayan faruwar lamarin.

Ana iya ganin wasu bangarorin jirgin kone kurmus yayin da bakin hayaki ya turnuke sararin samaniyar inda lamarin ya faru.

Har yanzu ba a san musabbabin faduwar hadarin ba, amma kafofin watsa labaran cikin gida na bayar da rahoton cewa mai yiwuwa tsuntsaye ne suka shige cikin injin jirgin suka haifar masa da matsala.

Karanta Wannan  Kalli Kayatattun hotunan Rahama Sadau

Kawo yanzu dai an samu mutane biyu da ransu, kuma ana ci gaba da aikin ceto, kamar yadda wani jami’in kashe gobara ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Yanzu haka jami’an agajin gaggawa na ta kokarin ceto mutanen da ke can baya, wato karshen jirgin, in ji wani jami’in filin jirgin.

Shugaban ƙasar na riƙo ya aike da saƙon jaje ga ‘yan ƙasar, tare da alƙawarta gudanar da bincike.

Hukumar sufurin ƙasar ta sanar da jigilar mutane a jiragen ƙasa kyauta zuwa wurin da lamarin ya faru.

Iyalai da ‘yan’uwan wadanda lamarin ya shafa sun yi cincirindo a wajen filin jirgin saman cike da faragabar rasa ‘yan’wansu.

Karanta Wannan  Majalisar Najeriya na neman bahasi kan yawan lalacewar jirgin Abuja-Kaduna

‘Na’urar kula da filin jirgin ta buƙaci direban ya jinkirta sauka saboda tsuntsaye’

Jami’an hukumar sufurin Koriya ta Kudu sun bayar da bayanai kan abin da ya faru da jirgin yayin da ya doshi filin sauka.

Da farko jirgin ya yi yunƙurin sauka, amma sai na’urar da ke kula da filin jirgin ta aike masa saƙon ya jinkirta sakamakon tsuntsaye da ke shawagi a titin da zai sauka.

Minti biyu bayan gargaɗin da aka aike wa jirgin, sai direban ya yi kiran gaggawa ga na’urar kula da filin, wanda ta ba shi damar sauka, amma ta ɗaya gefen.

Nan take direban ya amince ya kuma sauke jirgin.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 19 wajan kula da jiragen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a cikin watanni 15 da suka gabata

Bidiyon saukar jirgin ya nuna yadda ya sauka ba tare da tayoyi ko wani abu da ke taimaka wa saukar jirgi ba, lamarin da ya sa ya kauce wa hanyar har ya je ya bugi wani gini kafin ya kama da wuta.

Ma’aikatar sufurin ƙasar ta ce direban jirgin ya jima yana tuƙin jirgin sama tun 2019, yayin da ya shafe fiye da sa’o’i 9,800 yan tuƙa jirgin sama.

Tuni dai kamfanin da ya mallaki jirgin saman ya aike da saƙon neman afuwa da iyalan mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Wannan haɗarin jirgin sama na faruwa ne kwanaki kadan bayan wani makamancinsa da ya faru da wani jirgin saman Azerbaijan, da ya janyo mutuwar mutane 38, da jikkatar wasu da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *