Tuesday, January 7
Shadow

Hisbah ta fara kwashe yaran da ke gararamba kan titunan Kano

Gwamnatin Kano ta fara kwashe ‘dubban’ yara da ke rayuwa a kasuwanni da ƙasan gadoji a Kano, babban birnin jihar.

Gwamnatin ta fara ɗaukar matakin ne a jiya Litinin, inda ta samar da wani sansanin ajiyewa da kuma tantance yaran.

Shugaban hukumar Hisbah a jihar, Sheikh Aminu Daurawa ya ce “mun samu rahoton akwai ɗaruruwa ko kuma dubban ƙananan yara da ba su haura shekara 15 ba waɗanda suke kwana a ƙarƙashin gadoji da cikin tashoshi da kuma kasuwanni.”

“Ci gaba da rayuwarsa a waɗannan wurare zai iya haifar da matsala ta tsaro da ta zamantakewa a nan gaba,” in ji Daurawa.

Shugaban na hukumar Hizba ya ce alƙaluman da suke da su sun nuna cewa akwai irin waɗannan yara masu gararamba a kan tituna sama da 5000.

Karanta Wannan  Hotuna: Wannan kyakkyawar budurwar na neman mijin aure, tace a taimaketa

Ya kuma bayyana cewa za a tara yaran da aka kwashe ne a wata cibiya, inda za a tantance su, sannan a san matakan da za a ɗauka.

Kano ce jiha mafi yawan al’umma a arewacin Najeriya, kuma ɗaya daga cikin waɗanda ke da yawan ƙananan yara waɗanda ba su zuwa makaranta.

Duk da cewa jihar na daga cikin waɗanda suka sanya hannu kan dokar kare hakkin yara a Najeriya, amma har yanzu akwai dubban yara da ke tallace-tallace ba tare da zuwa makaranta ba, yayin da wasu yaran kuma ke barace-barace a kan tituna da sunan neman ilimin addini.

Sheikh Daurawa ya ce bayan kammala tantance yaran, da inda suka fito, za a sanya wasu daga cikinsu makaranta yayin da za a koya wa wasu sana’a.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna da Bidiyon gida na farko da aka gina shi sama a kasa a Najeriya

Ya kuma bayyana cewa akwai yiwuwar gurfanar da wasu iyayen da aka tsinci yaran nasu na gararamba kan titi, a gaban kotu.

“Wanda ya yi sakaci ya bar ɗansa yana yawo a kan titi duk da cewa yana da halin ɗaukar nauyinsa, to za mu gurfanar da shi a gaban kotu”.

Sai dai ya ce yaran da ba su da iyaye ko waɗanda rikici ya tarwatsa – gwamnatin za ta ɗauki matakin gyara musu rayuwa ta hanyar ba su ilimi da koya musu sana’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *