Wednesday, January 8
Shadow

Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina za su kafa tashar talabijin

Kafofin yaɗa labarai a Nijar da Mali da Burkina Faso sun ruwaito a ranar Litinin cewa ƙasashen za su kafa wata tashar talabijin ta intanet da zimmar “ƙarfafa haɗin kai da kuma yaƙi da labaran ƙarya” a yankinsu na Sahel.

Ƙasashen uku da sojoji ke mulki, sun kafa ƙawance da suka kira Alliance of Sahel States, wanda suke kira da Aes a Faransanci.

“Ana sa ran tashar za ta inganta harkokin sadarwa tsakanin ƙasashen Sahel kuma a samu tasiri mai ɗorewa bisa muradin shugabannin ƙasashen biyu,” in ji rahoton shafin Actu Niger.

An ƙulla ƙawancen ne a 2023 bayan sun sanar da aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas, wadda suka zarga da yi wa ƙasashen Yamma aiki.

Karanta Wannan  TIRƘASHI: Muna Ƙara Faɗa Ba Za Mu Yi Juyíɲ Mulki A Najeriya Ba, Céwar Shugaban Sojoji

Nijar da Mali da Burkina duka sun yanke alaƙa da ƙasashen Yamma kamar Faransa kuma suka maye gurbinta da Rasha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *