Wednesday, January 8
Shadow

Kalli Bidiyo da Hotuna: Kungiyar B0k0 Hàràm ta kaiwa Sansanin Sojojin Najariya hari ta kashe sojoji 7

Kungiyar ISWAP data balle daga jikin B0K0 Hàràm ta kaiwa sansanin sojojin Najariya hari a garin Damboa dake jihar Borno.

Maharan sun kona gidaje da motocin sojojin da kashe akalla sojoji 7.

Rahoton Sahara Reporters yace maharan sun shafe awanni 2 suna cin karensu ba babbaka a sansanin sojojin.

Rahoton yace harin ya farune ranar 4 ga watan Janairu, watau Asabar data gabata.

Wani soja yace zuwa yanzu sun gano gawarwakin Sojoji 7, kuma ya kara da cewa an kai musu harinne da misalin karfe 4 na safe.

Kalli Bidiyon anan

Karanta Wannan  Bankin Duniya ya gargadi Shugaba Tinubu kada ya sake ya dawo da tallafin man fetur inda yace idan aka ci gaba da biyan tallafin kasar zata fada bala'i

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *