Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, wadda tsohuwar matar Sani Musa Danja ce, ta bayyana hakan cikin wani bidiyo da ta wallafa.
A cikin bidiyon ta bayyana yadda mata ke shiga mawuyacin hali bayan mutuwar aurensu.
Ta shawarci mata da su kasance masu haƙuri a gidajensu na aure tare da gujewa duk wani abu da ka iya kawo musu ɓaraka da mazajensu.
Ta yi gargaɗin cewa babu komai a rayuwar zawarci sai tarin baƙin ciki da da-na-sani.
Me za ku ce?