Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa ta Najeriya ICPC ta maka kwamishina a tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna, Bashir Saidu a kotu bisa zargin almundahanar kuɗi.
Jami’in shari’a na hukumar ICPC, Osuobeni Akponimisingha ne ya gabatar da ƙarar a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Talata, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Takardar ƙarar mai lamba FHC /KD/IC/ 2025, ta nuna cewa an maka Bashir Sa’idu a kotun ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka danganci almundahana da rashawa.
A wani rahoto da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar a bara, ta zargi tsohuwar gwamnatin da almundahanar sama da naira biliyan 423 na jihar.