Thursday, January 9
Shadow

Bankin China ya bai wa Najeriya rancen kuɗin gina titin jirgi kasa daga Kano zuwa Kaduna

Bankin raya ƙasa na China ya bai wa Najeriya rancen dala miliyan 254.76 domin gina titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna.

Sanarwar da bankin ya fitar na zuwa ne gabanin ziyarar ministan harkokin wajen China a Najeriya cikin mako mai zuwa.

Minista Wang Yi zai isa Najeriya domin ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya tun daga ranar Laraba.

Aikin layin dogon mai tsawon kilomita 203, ana sa ran zai laƙume dala miliyan 973 amma ya dakata saboda ƙarancin kuɗi.

“Idan aka kammala shi, layin dogon zai haɗe Kano, mai muhimmanci a arewacin Najeriya, da kuma Abuja babban birnin ƙasar, inda zai ba wa mutane damar yin tafiya mai sauƙi,” a cewar sanarwar da bankin ya wallafa a shafinsa na intanet.

Karanta Wannan  'Gwamnatin tarayya za ta yi cikakken bincike kan harin ƙauyukan Silame'

Tun da farko gwamnatin Najeriya ta ce Exim Bank na China zai ɗauki nauyin aikin a 2020, amma sai ya janye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *