Sunday, May 18
Shadow

Mutane 573,519 ne suka nemi aikin Kwastam wanda ma’aikata 3,927 ne kadai za’a dauka

Hukumar Kwastam ta sanar da cewa mutane mutane 573,519 ne suka cike bayanai na neman aikin data bude ta kafar yanar gizo.

Hutudole zai iya tunawa cewa ministan kudi, Wale Edun yace an amincewa hukumar ta Kwastam ta dauki karin ma’aikata 3,927.

Hakan na nufin daga cikin mutane 573,519 da suka nemi aikin, guda 3,927 ne kadai za’a dauka aikin.

Me magana da yawun hukumar ta Kwastam, Abdullahi Maiwada ne ya bayar da karin haske akan lamarin inda yace adanda suka nemi aikin sun hada da masu digiri da Diploma da takardar kammala Sakandare.

Karanta Wannan  Zan Yi Tattaki Daga Jihar Gombe Zuwa Abuja Domin Kaiwa Maulana Prof. Ibrahim Maqari Ziyara, Inji Rumanatu Sa'ad Abubakar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *