Thursday, January 9
Shadow

Ka dakatar da shirin shigo da kayan abinci daga kasar waje, saboda tabbas farashin kayan abinci zai yi sauki amma mu kuma kasuwancin mu zai lalace>>’Yan kasuwar Najeriya suka roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shan matsin lamba akan lallai sai ya dakatar da cire harajin da yace zai yi akan kayan abinci da na magani da sauransu da ake shigowa dasu daga kasashen waje saboda kayan su yi sauki, ‘yan Najeriya su siya da Arha.

Majiyoyi da yawa daga fadar shugaban kasar sun tabbatar da wannan batu inda suka ce ‘yan kasuwa da kamfanoni masu zaman kansu ne suke matsawa shugaban kasar akan lallai ya janye wannan abu da yake son gudanarwa.

Suna bada dalilin cewa idan shugaban yace sai yayi hakan, to lalai zai dakushe zuba jari a Najeriya kuma za’a rasa ayyukan yi.

Karanta Wannan  GWANIN SHA'AWA: Yadda Kiristoci Suke Gadin Musulmai Suna Sallah A Yayin Źanga-Źanģàr Tsadar Rayuwa A Garin Jos

Hakanan wasu daga cikin kamfanonin da ‘yan kasuwar sun tabbatar da wannan batu inda suka ce idan shugaban kasar ya cire harajin aka fara shigo da kayan daga kasashen waje suka yi sauki a Najeriya, to su kuma kasuwancinsu zai durkushe.

Majiyar daga fadar shugaban kasa ta gayawa jaridar Punchng cewa, gidajen jaridu da yawa na ta sukar shugaban kasar kan kin aiwatar da wancan tsari na shigo da kayan abinci ba tare da haraji ba, amma abinda basu sani ba shine kungiyoyin ‘yan kasuwa da kamfanoni ne suke bada shawarar kada ayi hakan.

Sunc maimakon bari a shigo da kayan abinci daga kasashen waje da magunguna ba tare da haraji ba, kamata yayi a karfafa wanda ake dasu na gida kuma a kara samar da wasu.

Karanta Wannan  Ana rade-radin akwai yiyuwar wasu manyan jami'an gwamnatin Tinubu su yi Murabus

Tun ranar 10 ga watan Yuli na shekarar 2024 ne dai ministan noma, Abubakar Kyari ya bayyana shirin cire haraji akan kayan abinci da ake shigowa dasu daga kasar waje da suka hada da Alkama, Masara, Shinkafa da sauransu.

Sannan kuma ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin tarayya zata shigo da Masara da Alkama dan sayarwa a farashi me sauki.

Saidai tun bayan waccan sanarwar ba’a kara jin wani karin bayani kan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *