Friday, January 10
Shadow

Gwamnatin Bauchi ta ware Naira miliyan 400 don sayen kwamfuta guda shida ga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ware Naira miliyan 400 a cikin kasafin kudin shekarar 2025 don sayen kwamfuta guda shida domin ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar.

Jaridar The Guardian ta rawaito cewa, haka kuma, gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan daya don “sayen fili domin gina ofisoshi da gine-gine.” Za ta kuma kashe Naira miliyan 170 don sayen janareta domin samar da wutar lantarki a ofishin SSG.

Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Ibrahim Musa, ya soki wannan kasafi, yana mai bayyana shi a matsayin rashin fifikon abubuwan da suka dace a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da wahalhalu sakamakon manufofin tattalin arzikin gwamnati.

Karanta Wannan  Shugaban 'Yansandan Najeriya ya bayar da umarni ga 'yansanda su daura bakin kyalle dan nuna Alhinin rayuwar shugaban sojoji

Musa ya bukaci Gwamnatin Jihar Bauchi da ta kauce wa yin hakan tare da mayar da hankali kan ayyukan da za su kawo ci gaba a rayuwar al’ummar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *