Yaran da aka sace daga jihar Bauchi su 3 zuwa Jihar Anambra an mika su hannun iyayensu bayan kubutar dasu.
A shekarar 2024 ne dai mutumin da ake zargi ya sacesu.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, Auwal Musa ne ya mika yaran ga gwamna Bala Muhammad na jihar ranar Laraba.
Daga nan ne shi kuma gwamnan ya mika su hannun iyayensu.